Hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta bayyana bankado wasu kamfanonin dillalan aikin hajji da karbar kudi suna nuna cewa za su kai alhazai don gudanar da aikin hajjin bana.
Hukumomin tashoshin teku na wasu kasashen Afirka ta yamma sun daura damarar yaki da barayin teku da ke barazana ga lamuran kasuwancin teku a yankin.
Ma'abota lamuran zabe da siyasa na cewa dawo da hakkin gudanar da zaben fidda gwani hannun hukumar zabe ne zai gyara harkar dimokradiyya a Najeriya.
Tsawon yajin aikin ma'aikatan sashen shari'a a Najeriya ya kawo koma baya ga lamuran adalci don yadda rashin zaman kotuna ya bar wadanda a ke tuhuma da dama a gidajen yari ko ofisoshin 'yan sanda.
An kada kuri'ar dawowa daga rakiyar gwamnatin Buhari yayin da mutane kuma su ka gwale Sanata Sa'idu Dansadau da ya yi wuf ya amshe bututun magana daga Imam Ibrahim Auwal Usama.
Shugaban gungun barayin da su ka sace daliban jami'ar Greenfield a Kaduna Sani Idris Jalingo da a ka fi sani da "Baleri" ya yi barazanar hallaka sauran daliban matukar ba a turo Naira miliyan 100 da baburan Boko Haram 10 ba.
Rahotanni daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa, an sake sako wani rukunin dalibai biyar daga cikin 'yan makarantar kwalejin horar da ilimin gandun daji da aka sace a watan jiya.
Kundin tsarin mulkin Najeriya na cike da dokoki masu ma'ana da la shakka in an yi amfani da su, za su tabbatar da adalci da galabar masu amana kan maciya amana.
Shirin “Arewa A Yau,” Ci gaban inda muka tsaya ne a makon jiya, inda za ku ji sauran sharhi ko ra’ayin Attahiru Baburawa kan kalaman batun odar makamai da mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Manjo Janar Babagana Monguno ya yi magana akai.
Masu gabatar da jawabai a taron kaddamar da wasu littattafai na adabi sun bayyana cewa yawan saki da ake yi a aure a Arewa, na daga cikin manyan dalilan da ke haifar da matsalar 'yan bindiga dadi da ma 'yan ta'adda.
Mako biyu kacal gabanin azumin watan ramadna na bana hijra 1442, malamai da sauran jama'a sun taru a dakin taro na masallacin tarayya a Abuja don kaddamar da faifan karatun alkur'ani mai girma izu 60 da Imam Abbas Uzairu Chikaji Zaria ya karanta.
Tashoshin dakatar manyan motoci sun fara aiki don rage yawan hatsari da ke faruwa a sanadiyyar gajiya da direbobi ke samu a Najeriya.
Ma'abota son a yi sulhu a matsayin mafita ga tabarbarewar tsaro a yankin arewa sun gudanar da wani taro a Kaduna.
Kalaman mai ba wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, da ya shafi tsoffin manyan hafsoshin soja kan batun rashin ganin makamai da aka sata da makudan kudaden da ake warewa ya janyo martani daga jama'a.
Muhawara ta sarke tsakanin gwamnatin Najeriya da jihar Delta da ke kudancin kasar kan hakkin kashe kudin da tsohon gwamnan jihar, James Ibori ya sace da Burtaniya za ta maido wa Najeriya.
Hadaddiyar kungiyar fataken abinci da dabbobi ta Najeriya, ta jaddada dalilinta na kin janye yajin kai abinci kudancin kasar.
Domin Kari