Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Naira Ta Rikito Kasa A Kasuwar Canji Kan Dalar Amurka


Kudaden Naira
Kudaden Naira

A baya, babban bankin Najeriya ya daina ba da dala ga kasuwar canji inda ya bukaci duk mai son dala ya nufi bankin sa don samun ta kan farashin hukuma.

Bayan samun tsawon mako Naira na tsaya a farashi daya wato Naira 565 kan dalar Amurka yanzu ta samu koma baya na bazata. A binciken farashi a kasuwar canji a Lagos a farkon makwan nan na nuna yanzu dala daya na tashi kan Naira 572. Wannan na neman dusashe hasashe ko fatar wasu masu sharhi cewa dalar zuwa karshen shekarar nan za ta fado tun da a watan jiya ta sauko zuwa Naira 540 har ma kasa da hakan wato wajen 530. In aka debe karin farashin man fetur, baa bun da kan zama dalilin tashin farashin kayan masarufi a Najeriya irin tashin farashin dala kan Naira. A baya, babban bankin Najeriya ya daina ba da dala ga kasuwar canji inda ya bukaci duk mai son dala ya nufi bankin sa don samun ta kan farashin hukuma.

XS
SM
MD
LG