Da alamu cibiyar ta dau wannan matakin ne don yanda gine-gine ke rugujewa musamman bayan rugujewar gini mai hawa 21 a Ikoyi Lagos a watan jiya.
An tabbatar da wannan cibiya ta zama bisa doka a 2018 inda ta ke da hurumin ba da lasisi ga dukkan kwararrun da ke jagorantar ayyukan kwarewa da kuma hukunta wadanda ba su da lasisi ko su ka jagoranci ayyuka marasa inganci.
Da zarar ‘yan Najeriya sun fahimci aikin wannan cibiya, za su rika daukar jami’an da za su kula mu su da ayyuka da ke lasisin cibiyar, don in jami’in kwangila ya yi shirme a janye lasisin sa” inji shugabar cibiyar Victoria Okoronko da take magana a taron manema labaru a Abuja.
Okoronkwo ta sake cewa za su tabbatar da aiwatar da hakkin da doka ta dora akansu don ganin an hukunta duk wanda ya saba ka’idar aiki.
Mataimakin shugaban cibiyar na Arewacin Najeriya Dr. Jamilu Isa ‘Yankwashi ya ce dokar ba za ta kyale hatta wanda ya dau jami’in kula da kwangila da ba kwarerre ba.
Sau da dama a Najeriya a kan samu jami’an da ke kula da manyan ayyuka da ke aiki da takardun jabu ko kuma dama haye su ka yi ba koyo ba.
Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-Hikaya: