Idan za a tuna gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya zargi mai dandalin dan Najeriya mazaunin Burtaniya Olumide Oniwinde da tada farashin dala da sauran kudin ketare ta hanyar ba da farashin da ya wuce ka’ida a shafin na sa da mutane kan dogara da shi don sanin yadda canji ya kwana.
A daidai lokacin da Emefiele ya yi barazanar da ta sanya shafin Aboki FX rufe sashin bayanan canjin Naira ya koma na kudin yanar gizo wato Cryptocurrency an kara samun tashin farashin dalar da wajen Naira 5 don in ba wani abu ne ya canja a wunin ranar Litinin ba, dala daya ta kama Naira 565 ne a kasuwar bayan fage.
Emefiele da tuni ya dakatar da bada dala ga kasuwar canji, na karfafa lalle mai son dala ya tunkari bankin sa da sahihan takardun tafiya, na magani ko kasuwanci don samun kudin bisa canjin gwamnati.
Hakanan idan ma bukatar mutum ta wuce mizani za a iya sanar da babban bankin don dubawa a biya bukatar mai bukata.
‘Yan kasuwar canjin a Abuja na ci gaba da harkokinsu cikin natsuwa da fatan gwamnati ta sauya tsari don cigaba da sako dalar maimakon dogaro ga masu fito da ita daga ma’ajiyar banki ko gida su na sayarwa don samun na kashewa.
Dan canji Jibrin Zakar ya ce ba mai son tsadar kuma su ma ‘yan canji na iya asara ko riba ga yadda dalar ba ta da tabbas.
Masanin tattalin arziki a Abuja, Yusha’u Aliyu, ya ce matakan na gwamnati kan kasuwar canji ba za su zama da illar gaske ba inda a gefe a na lura da gaskiyar wadanda kan samu dalar daga bankuna.
Ba a taba samun tashin dala a tarihi da ya kai wannan karo ba don ko lokacin da lamarin ya yi muni a wajajen 2015 farkon hawa mulkin shugaba Buhari, ta cilla zuwa N520 amma zuba dala a kasuwar canji ta sauko da ita zuwa kasa da Naira 400.
Saurari cikaken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya: