Fiye da shekaru shida bayan majalisar dokokin Najeriya ta amince da kudurin dokar dake bada kariya ga iyalai, musamman mata da yara, daga dukkanin nau’ukan cutarwa, har yanzu masu ruwa da tsaki na fafutukar ganin gwamnatin jihohin sun kafa tare da zartar da samfurin wannan doka a jihohin su.