Shugaban hukumar ta NAPTIP Sanata Bashir Lado wanda ya jagoranci kaddamar da kwamitin a Kano yace, daukar matakin ya zama wajibi la’akari da cewa, shiyyar Kano tayi iyaka da wasu sassa na Jamhuriyar Nijar kuma miyagu na amfani da ita wajen safarar ‘yan Najeriya zuwa kasashen Libya da nahiyar turai.
Danmajen Kano wanda shike wakilatar masarautar Kano a cikin kwamitin yace masarautun Kano ba za suyi wata wata ba wajen bada baya nan da ake bukata domin kakkabe masu akidar safarar bila’dama.
Haka kuma Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yace gwamnatin Kano tayi maraba da nuna farin ciki ga wannan yunkuri musamman dangane da gidaje ko gine-ginen da ake amfani dasu wajen boye wadanda ake yunkurin safarar su zuwa ketare kuwa, gwamnan yace.
Kimanin ‘yan najeriya 150 ofishin shiyyar Kano na hukumar NAPTIP ya ceto daga hannun masu safarar mutane cikin kasa da makonni 4 da suka shude, lamarin dake nuna yawaitar masu wannan ta’ada a Najeriya.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: