Sai dai wasu majiyoyi a gidan gwamnatin Kano sun tabbatar da cewa, hukumar ta EFCC ta gayyaci matar Gwamnan Hajiya Hafsa Umar Ganduje, domin amsa tambayoyi kan korafin da danta Abdul'aziz Ganduje ya mikawa hukumar.
Tun farko dai wasu jaridun Najeriya ne suka wallafa labarin cewa mai dakin gwamnan Kano Hafsat Umar Ganduje ta bakunci shalkwatar hukumar ta EFCC a ranar Litinin domin amsa wasu tambayoyi game da zargin amfani da gwamnati wajen azurta kai ta hanyar hada-hadar filayen gwamntin.
Kamar yadda jaridun suka ruwaito Hajiya Hafsa Ganduje ta na tsare a shalkwatar hukumar EFCC, kuma kuma ranar Talata ake tsammanin za ta ci gaba da amsa tambayoyi daga jami’an hukumar.
Sai dai gwamnatin jihar Kano ta musanta wannan batu, amma ta tabbatar da cewa, Hafsat Umar Ganduje na tare da mai gidanta a can Abuja.
Sai dai kwamishinn labaru na jihar Kano, Comrade Muhammad Garba ya tabbatar da cewa, Hajiya Hafsat Ganduje tana Abuja, duk da yake wasu rahotanni na cewa, da sanyin safiyar ranar Talata ta bayyana a Kano.
Kakakin shiyyar Kano na hukumar EFCC Malam Idris ya ce ba shi da masaniya dangane da wannan batu la’akari da cewa, dama tun fari an gabatar da batun a shalkwatar hukumar dake Abuja.
Shi kuwa kakakin hukumar EFCC na kasa Mista Wilson Uwajoren, wayar sa a kashe take kuma bai amsa sakon karta kwana da aka aika masa ba kan wannan rahoto.
Kimanin makonni biyu da suka gabata ne hukumar ta EFCC ta ayyana neman maidakin gwamnan na Kano, biyo bayan takardar korafi da danta Abdul’aziz Ganduje ya mikawa hukumar.
A cikin takardar, Abdul’aziz Ganduje ya yi ikirarin cewa, ya yi silar mu’amalar kudi ta dubban dala tsakanin mai dakin gwamnan da wani dan kasuwa dake muradun mallakar wasu filaye a Kano.
Abdul’aziz ya ce bayan kimanin watanni uku da bada kudaden, batun samar da filayan ya ci tura, al’amarin daya sanya dan kasuwar ya nemi kudinsa su dawo gida.
Rashin cimma nasara akan haka, ya sanya shi Abdul’aziz ya mika maganar ga hukumar EFCC.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari: