Rahotan da bankin duniyar ya wallafa ya ce duk kokarin da hukumomin Najeriya karkashin gwamnatin Muhammadu Buhari ke cewa suna dauka domin ceto tattalin arzikin daga komada, alkaluman nazari da binciken da bankin na duniya ya yi sun tabbatar da yanayin garari da tattalin arzikin ke ciki.
Rahotan ya ce yayin da tattalin arzikin na Najeriya ke kara shiga cikin nayin komada, a hannu guda kuma kasar na fuskantar karuwar yawan jama’a cikin sauri.
Akalla gwamnatin Muhammadu Buhari ta ciyo bashin ketare kusan sau biyar daga cibiyoyin ketare irin su bankin duniya, a kokarinta na ta da komadar tattalin kasar duk kuwa da tsauraran sharrudan da ake cewa cibiyoyin na gindayawa kasashen dake karbar lamunin.
Amma wani mai sharhi Dr. Lawan Habib Yahya ya ce gwamnati tana daukar matakin gyara kamar yadda rahotan na bankin duniya ya ambata.
Rahotan na bankin duniya ya nuna cewa rabon Najeriya ta fuskanci mawuyacin halin tattalin arziki irin wannan tun a shekarar 1987, yana mai cewa ala’mura sun fi zafafa a shekarar 2016 da kuma 2020 sanadiyyar annobar coronavirus.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari: