Sai dai kasa da watanni 24 wa’adin karshe na shugaba Buhari da galibin gwamnonin jam’iyyar ya kare, rigingimu a cikin jam’iyyar a matakai daban-daban a kuma jihohin daban-daban na ci gaba wakana.
Kwararru a fannin tsaro a Najeriya sun fara tsokaci akan yunkurin gwamnatin Kano na gudanar da aikin kidayar Fulani a jihar, a wani bangare na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar al’umar Jihar.
Da marecen jiya ne gwamnan na Kano ya yi wata ganawa da manema labaru a Kano kuma ya amsa wasu tambayoyi daga garesu.
Maniyyata aikin hajin bana da masu kamfanonin jigilar alhazai ta jirgin yawo a Najeriya na bayyana alhini dangane da sanarwar hukumomin Saudiyya na janye aikin hajji ga ‘yan kasashen waje.
Yayin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke umartar gwamnonin kasar su hada hannu da masu rike da sarautu da shugabannin kananan hukumomi domin tabbatar da tsaro a yankunansu, karamar hukumar Ungogo a jihar Kano ta kaddamar da cibiyar yi wa Jama’ar yankin rijista.
Yayin sauraron ra’ayoyin jama’ar shiyyar arewa masu yammacin Najeriya kan gyaran kundin mulkin kasa, batun tsaro shi ne ya fi daukar hankali sai kuma sauran muhimman batutuwa domin samar da ci gaba a kasar.
Gwamnatin Najeriya ta ce duk da biliyoyin Naira da ta fitar karkashin tsare-tsarenta na yaki da fatara ta hanyar tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu da sana’oi, domin bunkasa tattalin arziki daga tushe, matsalar annobar coronavirus ta haifar da koma baya ga cimma wannan buri.
Hukumomin tsaro a Kano sun haramtawa Fulani makiyaya shiga Jihar ba tare da takardun da ke fayyace daga wurin da suke da kuma yankin da za su sauka ba.
Yau aka shiga rana ta biyu da fara taron kungiyar Malaman koyar da ilimin aikin Jarida da yada labarai ta Nahiyar Afrika, wato African Council for Communication Education dake gudana a Kano.
An shiga rana ta uku da zaman zullumi a kayuka da garuruwatakwas na yankin karamar hukumar Kirikasamma ta a jihar Jigawa dake yamma maso arewacin Najeriya biyo bayan rikici Tsakani manoma da Fulani makiyaya a yankin.
Yayin da Jami’an kiwon lafiya ke ci gaba da kula da fiye da mutane 70 da hadarin gobara ya ritsa da su a gidan sayar da man fetir na Al-ihsan dake kan titin Sharada a birnin Kano, hukumomin kashe gobara a jihar na danganta lamarin da rashin kiyaye ka’idoji daga bangaren mamallaka gidan man.
Hukumar bunkasa ilimin fasahar sadarwa ta Najeriya NITDA ta rattaba hannu akan daftarin yarjejeniyar aiki tare da cibiyar MassChallenge mai kula da harkokin fasahar sadarwa dake Amurka, domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta wannan fuska.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke cewa ya kamata hukumar ta NITDA ta warware wasu kalubale da suka shafi ayyukanta.
Manoma a Najeriya sunce aikin daminar bana zai fuskanci mummunar barazana fiyeda ta shekarun baya, saboda kalubalen tsaro da kasar ke fama da shi.
Gwamnatin Najeriya ta ce shirinta na bunkasa fannonin tattalin arziki marasa alaka da bangaren mai, na haifar da sakamako mai kyau ta fuskar habaka tattalin arzikin kasar.
Gwamnatin jihar Kano ta ranto kusan naira biliyan tara daga babban bankin kasar domin bada kwangilar gina gada ta zamani a mashigar birnin Kano ta bangaren gabas.
Gwamnatin jihar Jigawa a Najeriya tace tana dakon shawarwarin kwararru akan rahotan da Majalisar Dinkin Duniya ta wallafa, inda ta bukaci mahukunta su sauyawa garin Hadejia matsugunni saboda barazanar ambaliyar ruwa da garin fuskanta a kowace shekara.
Yayin da hukumar NITDA dake bunkasa ilimin fasahar sadarwa a tsakanin ‘yan Najeriya ke cewa ta dukufa wajen samar da cibiyoyin koyo da kuma amfani da kayayyakin fasahar sadarwa a birane da yankunan karkara, masu sharhi kan lamuran tsaro na kokawa kan karancin amfani da na’uorin fasahar zamani.
Wasu kalamai da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi dangane da raba filaye da gwamnatin APC mai ci take yi, sun sa masu sharhi shiga yin lissafin abin da ka iya faruwa a zaben 2023.
Lokacin da shugaba Buhari ya dare kujerar mulki a shekara ta 2015, ya gaji farashin litar man fetir akan naira 87 amma yanzu ana sayar da ita naira 165 kuma ana hangen za a kara farashin man a kwanan nan.
Domin Kari