Alkalin babbar kotun Kanon mai shari’a Nura Sagir yace bayar da umarnin, nada nasaba da la’akari da korafin da mallamin ya yi cewa, gabanin rufe makaranta da masallacin nasa, kotun majistiren ba ta bashi damar kare kansa game da wasu tuhume tuhume da ake yi masa.
Kakakin kotunan Kano Baba Jibo Ibrahim ya yi karin bayani game da wannan batu akan cewa babbar kotun ce ta ba da umarnin su shigar da wannan karar.
Yanzu haka dai kotun ta sanya 27 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da zata yi zaman sauraron hujjojin da lauyoyin Malam AbdulJabbar din suka shigar.
Sai dai ta umarci kotun majistiraren mai lamba 12 karkashin jagorancin mai shari’a Mohammed Jibrin da bangaren shi AbdulJabbar Nasiru Kabara da su dakata da komai har sai ta kammala sauraren abin da aka mika gabanta.
Karin bayani akan: jihar Kano, AbdulJabbar Nasiru Kabara, Mohammed Jibrin, Nigeria, da Najeriya.
Barrista Rabi’u Shuaibiu Abdullahi dake kare Malam AbdulJabbar a wannan shari’a yace ba zasu ce komai ba a wannan karon, sai dai watakila nan gaba.
Hakan dai na zuwa ne kasa da makonni biyu bayan da zauren hadin kan malaman Kano ya ce ya rubutawa gwamnati wasika har sau uku domin jin inda aka kwana game da wannan batu, a cewar sakataren zauren Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa.
Tun fari dai gwamnatin jihar Kano ce ta nemi umarnin kotun majistiraren jihar Kano, karkashin mai shari’a Mohammed Jibrin ta rufe masallacin Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara da hana shi taron wa'azi, har sai jami’an tsaro sun kammala bincike.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari: