Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iyayen Yaran Da Aka Sace A Kano Sun Yi Maraba Da Hukuncin Kotu


Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano
Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano

Iyayen yaran nan da aka sacewa 'ya'ya a Kano kuma aka yi safarar su zuwa jihohin Anambra da Enugu da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya sun yi maraba da hukuncin da babbar kotun Kano ta yanke na shekara 104 a gidan gyaran hali.

Sai dai iyayen yaran sun roki gwamnatin Kano da ta kara kaimi wajen neman sauran yaran da har yanzu ke hannun miyagu.

Jimillar caji 38 ne aka tuhumci Mr. Paul Owne guda cikin manyan masu kitsa yadda aka rinka satar ‘ya'yan mutane daga Kano kuma aka yi safarar su zuwa jihohin Anambra da Enugu, inda ake cinikayyar su tare da sauya masu suna da ma addini.

Bayan da kotun ta tabbatar da laifukan akan Paul kuma ya amsa dukkanin caji 38 din, alkalin Justice Zuwaira Yusuf Ali ta yanke hukuncin shekaru 104 a gidan yari ga Mr Paul.

La’akkari da kundin dokar hukunta masu satar mutane da safarar su, mai shari’a ta kasa jerin laifukan zuwa rukuni 3, inda kashi na daya dana 2 suka kunshi caji 12 kuma kowane ke dauke da hukuncin shekar 7, jimlatan shekaru 84 kenan.

Kana rukuni na uku na kunshe da caji 5 wanda kowane guda ke dauke da hukuncin shekaru 4 wato shekaru 20 kenan a gidan kaso.

Baya ga haka tilas Mr Paul ya biya tarar naira dubu 100.

Yanzu haka dai iyayen yaran sun bayyana farin ciki da wannan hukunci na kotu.

Sun kuma bukaci gwamnati ta kara kaimi wajen neman ragowar yaran su dake hannun miyagu, musamman batun gwajin kwayar halitta ta DNA da aka yi akan wasu.

Sauarari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:

Iyayen Yaran Da Aka Sace A Kano Sun Yi Maraba Da Hukuncin Kotu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00


XS
SM
MD
LG