Sai dai kwararru a fagen diflomasiyya sun ce hada karfi da karfe shi ne mafita. Hakan dai na zuwa ne a dai lokacin da masana kimiyya suka dukufa wajen gudanar da bincike akan sabon nau’in Omicron na kwayar cutar Corona.
Najeriya dai na cikin jerin kasashen duniya da aka samu rahotan bullar sabon samfarin cutar corona mai lakabin Omicron din, wadda yanzu haka kwararru a fannin kimiyyar cutuka da dakile yaduwarsu sun yin fashin baki tare da bincike a kanta.
Farfesa Isa Abubakar Sadiq shi ne Daraktan Cibiyar bincike da dakile cutuka masu saurin yaduwa ta Jami’ar Bayero Kano, ya kuma ce an gano ta a Afurka ta kudu wadda cutar kanjamau ta dade a jikinsu, sannan sai corona ta harbe su.
Wannan sabon nau’i na Korona mai lakabin Omicron, na neman haifar da takaddamar diflomasiyya a tsakanin kasashen Afurka da wasu kasashen nahiyar turai da Asiya, inda ya zuwa karshen makon jiya kasashen Canada, Burtaniya, Sjngapore, da kuma Indonesia suka dakatar da ‘yan Najeriya ko bakin da suka ziyarci Najeriya shiga cikin kasashensu saboda bullar samfarin Omicron na cutar Korona, al’amarin da Ministan lafiya na Najeriya Dr Osagie Ehanire ya bayyana a matsayin riga malam masallaci ne ga ayyukan hukumar lafiya ta duniya da kwararrunta.
Sai dai Ministan ya ce, galibin wadanda aka gano suna dauke da kwayar cutar bayan sun iso Najeriya daga Burtaniya suke.
Ya zuwa ranar Litinin din nan, an bada rahotan bullar nau’in Omicron na cutar Corona a kasashen duniya 23 wadanda suka fito daga nahiyar Afurka, Turai, Asiya da kuma India.
Saurari rahoton Mahmud Kwari: