Ana can ana kan fafatawa a gasar cin kofin zakarun Turai na kwallon kafa da a ke kira Champions Ligue.
Yanzu hankali ya karkata kan dauki ba dadin da ake kan yi tsakanin Man City da Real de Madrid. Man City dai ba ta daukar gamuwarta da Real de Madrid a matsayin abin wasa, tun bayan da Real Madrid ta mauje Chelsea.
Wannan karon, shirin labaran wasanni a takaice, ya karade sassa da dama. Hatta Jamhuriyar Nijer, inda wasu kungiyoyin kwallon kafa na mata su ka fafata.
Kirista a Jamhuriyar Nijer, sun ce ba za su yarda a yi banda su ba, wajen yi wa Nijer da Najeriya addu'o'i, kamar yanda hukumomin kasar suka nemi Musulmi su yi a cikin wannan watan azumin Ramadan na bana.
Wannan lamarin ya zo ne a daidai lokacin da a ke tunanin cewa, kura ta lafa a wannan garin na Illela.
“Duk wanda ya kai shekara daya har zuwa shekara 100 zai samu wannan magani.”
Al’umar Kiristoci a jamhuriyar Nijer sun dauki alwashin yin addu'o'i domin samun zaman lafiya da kawo karshen karshen matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta a kowane gefe.
Gwamnan Jihar Tahoua ya kai ziyara a babban asibitin birnin Jaha, domin gaida sojojin jamhuriyar Nijar da wadansu mahara da a ke zaton sun tsallako ne daga kasar Mali su ka jikkata a yankin Tilliya, a wani kazamin arangama.
Wadansu mutane da suka kai 50, dauke da manyan bindigogi ne, in ji mutanen garin Kwandamo a cikin karamar hukumar mulkin Illela ta Jihar Sokoto, da ke kan iyaka da birni N'Konni a Jamhuriyar Nijar suka kai harin.
An yi hawan idin babbar sallah a yau Talata a dukkan fadin kasar Jamhuriyar Nijar inda shugaban kasar Bazoum Mohamed da sauran mukarraban gwamnati da suka raka shi wurin wannan hawan idin babbar sallar a babban massalacin Kaddafi na babban Birnin Yamai.
Hukumomin jamhuriyar Nijer tarevda masu hannu da shuni dake tallafawa kasar a fannin kiyyon lafiya, suna shirya gangamin allurar rigakafin cutar shan'inna a jahohin Maradi - Tahoua da Zinder.
Daya daga cikin sarakunan Musulmi 4 Ali Zaki na Katsina Maradi ya rasu kamar yadda hukumomin jihar Maradi suka tabbatar wa manema labarai.
Dubun wadansu mahara masu garkuwa da mutane ta cika a garin Garu a karamar hukumar mulkin Illela ta jihar Sokoto da ke iyaka da Birni N'Konni a Jamhuriyar Nijar, yayin da wadansu suka kashe mutun guda a Araba dake da tazarar kilomita 2 da birni N'Konni.
Yau Laraba al’umomin Jamhuriyar Nijar suka yi karamar sallah biyo bayan sanar da ganin watan Shawwal, wanda ya kawo karshen watan Ramadan.
Majalisar koli ta addinin islamaa Nijar ta bayyana ganin jinjirin watan Shawwal dake nuna an kamalla azumin Ramadan na wannan shekara.
Yan ta'adda da ake kyautata zaton sun bullo daga kasar Mali ne, sun yi wa askarawan Nijar da ke sintirin tsaro da wanzar da zaman lafiya a yankin Tillia dake arewacin jahar Tahoua kwatan bauna, inda suka kashe soja 16
‘Yan bindiga sun yi barin wuta a garin Tunga da ke karamar hukumar Illela a jihar Sokoto, lamarin da ya sa mazauna garin gudun tsira da rayukansu zuwa makwabtan garuruwa.
Bayan binciken da gwamnatin jamhuriyar Nijer ta gudanar, ta ce ‘yan ta'adda da suka fito daga kasar Mali sun kai hare hare a cikin garuruwa da dama da wata tunga a cikin gundumar Tilliya ta jihar Tahoua inda su ka kashe mutane 137 wasu da dama kuma suka jikata.
Wadansu 'yan bindiga da a ke kyautata zaton masu tsattsauran ra'ayin addini ne da suka kutso daga kasar Mali, sun abka wa garuruwa 2 na gundumar Tilliya a cikin jahar Tahoua jamhuriyar Nijar, su ka kashe mutane 54.
Kotun kolin tsarin mulkin kasa ke da hurumin tabbatar da an kammala zabe, ba wani dan siyasa ba.
Domin Kari