Birnin Kwanni, Niger —
Yanzu haka dai, ana can ana kan fafatawa mafi zafi ta wassanin kusa da na karshe na kwallon kafa na zakarun Turai na champions ligue na bana tsakanin Man City ta Burtaniya, da Real de Madrid ta kasar Spain.
Kungiyoyin 2, sun dai kai a wannan matsayin ne, bayan da Real de Madrid ta fidda Chelsea mai rike da wannan kambu kuma ke rike da kambun club - club na kwallon kafa na duniya, yayin da Man City ta gwabcekewa Athletico de Madrid.
Wassan na kusa da na karshe na Champions Ligue din na wannan shekara ta bana na 2, zai hada Villareal ta Spain a gobe Laraba da Liverpool ta kasar Burtaniya.
Kenan, a wannan shekara ta bana kungiyoyin kasashe 2 ne suka kai wannan matsayin na kusa da karshe wato Espagne ko Spain sai Ingila ko Grande Britagne.
Wassan karshe dai na bana na champions ligue na kwallon kafa na club club din da suka zama zakaru a kasashen Turai, zai wakana a ranar 28 ga Mayu a Stade de France a Saint Denis da ke kasar Faransa.
A wassanin kwallon hannu na tennis na duniya ko coupe davis, tuni a ka fitar da jadawalin wadannan wassanni na rukuni zuwa rukuni : Groupe A (à Bologne, ITA) : Croatie, Italie, Argentine et Suède. Groupe B (à Valence, ESP) : Espagne, Canada, Serbie et Corée du Sud. Groupe C (à Hambourg, ALL) : France, Allemagne, Belgique et Australie.
Groupe D (à Glasgow, GBR) : États-Unis, Grande-Bretagne, Kazakhstan, Pays-Bas.
Wadannan wassanin za su wakana ne, daga ranar 14 zuwa 18 ga watan Satumban wannan shekara da muke ciki ta 2022 a wadanan garuruwan da muka ambata a can baya.
Suko masu shirya wasanin tennis na Wimbledon na kasar Ingila, daya daga cikin wassani mafi girma na tennis na duniya na shekara - shekara, a yau Talata ne suka bada sanarwar cewa ba sai da takardun asibiti ba masu nuna cewa baka dauke da cutar korona kake iya halartar wannan kombalar cewa da yan wasa, abin da zai bai wa Novak Djokovic damar shiga wannan gasar daga ranar 27 ga watan Yuni zuwa 11 ga Yulin 2022.
Abin tuni dai shi ne, Novak Djokovic, bai samu damar shiga wassanin kwallon tennis na Australia na wannan shekara ba, saboda rashin wannan takardar gwajin ko yana dauke da cutar korona bairis ko a'a.
Shi dai dan kasar Sabia Novak Djokovic, shi ne ke rike da kambun wasannin na kwallon tennis na Wimbledon na kasar Burtaniya na shekaru 3 da suka gabata, abin da zai ba shi dama ta hanyar halartar wannan kombalar ta bana ta kare kambunsa.
Saurari rahoton Harouna Bako:
Kofin Duniya ta Qatar 2022
Nuwamba 01, 2022