Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Da 'Yan Ta'adda Suka Kashe A Jamhuriyar Nijer Sun Kai 137


Shugaba Mahamadou Issoufou
Shugaba Mahamadou Issoufou

Bayan binciken da gwamnatin jamhuriyar Nijer ta gudanar, ta ce ‘yan ta'adda da suka fito daga kasar Mali sun kai hare hare a cikin garuruwa da dama da wata tunga a cikin gundumar Tilliya ta jihar Tahoua inda su ka kashe mutane 137 wasu da dama kuma suka jikata.

A cikin daren jiya ne kakakin gwamnatin Jamhuriyar Nijer, Alhadji Zakariya, ya bayyana a kafofin yada labaran kasar domin sanar da ‘yan kasar a hukumance irin yanda ‘yan ta'adda su ka abka wa wadansu garuruwa da wata tunga a jihar Tahoua a cikin gundumar Tilliya har suka kashe mutane 137.

‘Yan ta'adda ne suka abka wa wadanan garuruwan na gundumar Tilliya su ka hallaka fararen hulla da ba su ji ba ba su gani ba.

Su dai wadannan 'yan ta'addar sun kai kololuwa wajen aikata danyen aiki, tun da ba su abka wa kowa sai fararen hulla, inji kakakin Gwamnatin kasar.

Ya ci gaba da cewa, gwamnati ta soma bincike domin gano wadanda su ka aikata wannan mumunan aikin, domin daukar matakin doka, ciki har da gurfanar da su gaban kuliya.

A cikin wannan mummunan yanayin, gwamnati ta kebe kwanaki uku na zaman makoki, kuma za a sauko da tutocin tsakiya, haka ma shugaban kasar da gwamnati na isar da sakon ta'aziyarsu ga wadanda suka yi rashi, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikata.

Haka ma, ta yi Allah wadai da danyen aikin wadannan ‘yan ta'adda, kuma ta na kira ga ‘yan kasar da su kiyaye da duk abin da ke kai komo, domin hukumomin Nijer sun lashi takobin ci gaba da yakar ‘yan ta'adda har sai sun cimma nasara.

Ga dai cikakken rahoton Harouna Mamane Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG