Sanadiyar yawaitar masu kamuwa da cutar amai da gudawa a birane da kauyuka a Jamhuriyar Nijar a kowace shekara musamman lokacin sauar ruwan sama, hukumomin kasarsun kaddamar da wani gagarumin yekuwar yin rigakafin cutar ta Cholera mai saurin kisa.
A shekaru baya-bayan nan ne yankuna masu tarin yawa a Jamhuriyar ta Nijar suka fuskanci annobar cutar ta amai da gudawa abin da ya sa hukumomin kasar kaddamar da wani gagarumin aiki.
An gudanar da rigakafin a birane da kauyuka yanzu haka ta hanyar bi gida zuwa gida.
Malam Assumane Abdu shine ke kula da hulda da jama'a a babbar assibitin Birni N'Konni.
“Duk wanda ya kai shekara daya har zuwa shekara 100 zai samu wannan magani.”
Su ma wadansu ‘yan kasa, sun bayyana gamsuwar su gameda wannan yekuwar da rigakafin cutar kolera a Nijer.
Wannan matakin da gwamnatin Nijar ta dauka, na yin gangamin rigakafin cutar ta Cholera zai taimaka wajen kawar da fargabar fadawa tarkon wannan cutar wacce ke sanadiyyar mutuwar mutane da dama a kasar.
Saurari rahoton Harouna Mamane Bako: