Zamu soma labarun wassaninmu na yau ne daga Jamhuriyar Nijer, inda kungiyar kwallon kafa ta mata ‘yan kasa da shekaru 17 ta kasa da ake kira Meina Nationale ta kara da kasar Morocco, da ta karkare ta da ci 11 da 0 a dandalin wasa na Stade General Seyni Kountche na Yamai, babban birnin kasar.
Wannan wasan na cikin tsarin tankade da rairaya na neman shiga gasar cin kofin duniya na kwallon kafa ta mata ‘yan kasa da shekaru 17 da za ta wakana a kasar India a wannan shekara ta 2022.
Kuma karawar, na cikin zagaye na 3, na neman shiga wannan kombalar ta mata ta kwallon kafa ‘yan kasa da shekaru 17 a yankin nahiyar Afurka.
Idan muka leka kasashen Turai kuma a jiya ne, kungiyar kwallon kafa ta Barca ta sha kashi a gida a hannun Cadix da ci 1 - 0.
Wannan kashin da Barca da sha a jiya a gida, ya kara jefa fargabata da ma tsoro ga magoya bayan kungiyar ta FC Barcelona dake tunawa da mawuyacin halin da kungiyar ta samu kanta a kakar kwallon kafa ta bana ta wannan shekara a kasar Spain, duk da yake, tun kama ragamar kungiyar da Xavi ya yi, ta samu ta farfadowa har ma tana ta 2 yanzu haka a teburin la Liga da maki 60 da kwantan wasa guda.
Ita ko Cadix da ta shamaci Barca a gida a jiya, yanzu haka, tana matsayin ta 16 da maki 31 a wassanin la Liga na Spain na wannan shekara ta bana.
Abin ya kara wa magoya bayan kungiyar takaici, bayan ta sha kashi a ranar Alhamis a Camp Nou a hannun 'Eintracht Francfort ta kasar Jamus a wassannin kwallon kafa na Europa Ligue na bana, inda kungiyar ta Jamus ta bantalike ta daga wannan gasar bayan ta zurde ta da ci 3 - 2. A cigaba da wasannin tennis na Barcelona na kasar Spain yanzu haka :
Humbert dan kasar Faransa, ya kai ga zagaye na gaba, bayan da yayi wa Nakashima dan kasar Amuruka ci 6 - 3, 6 -2. Sai Harris dan Ksar Brazil da yayi wa Carballes Baena dan kasar Spain, ci 6 - 4, 6 - 7.
Shi ma Kwan dan kasar Koriya ta Kudu ya sallami Benoit Paire dan Kasar Faransa da ci 6 - 4, 6 - 4. Sai da ma ta kai ga Benoit Paire din yin kaca - kaca da ragar buga kwallon na tennis dinsa, saboda wannan cin da a kayi masa da ke fidda shi daga wannan kombalar ta Barcelona ta kwallon tennis ta 2022.
Raphael Nadal dan kasar spain ne dai, ke rike da kamben wannan kombalar ta tennis bisa jan yashi, ko da yake, bai samu shiga kombalar ta bana ba saboda jin ciwo a kafa da ya yi.
Saurari rahoton Harouna Bako: