Lamarin da a ke zaton ‘yan kishin addinin Islama ne dake tsallakowa daga Mali.
Kwanaki 2 bayan wani hari da wata kazamar arangama da ‘yan ta'adda masu kaifiun kishin Islama suka kai wa dakarun jamhuriyar Nijar dake yankin Tilliya a Arewacin garin Aiza suna sintirin bada kariya ga al'ummar wannan yankin dake iyaka da kasar Mali da kuma wanzar da zaman lafiya a wannnan yankin, gwamnan jihar Tahoua, ya kai ziyara wa askarawan kasar da suka jikatta a babbar assibitin garin Tahoua, birnin Jaha da asibitin barikin sojoji, inda yayi masu jinjina ta musaman kamin yayi musu fatan alheri da samun waraka.
Hukumomin jamhuriyar ta 7 da askarawan wannan kasar sun dage ba gudu ba ja da baya na sai sun kakkabe ta'adanci, kuma sun ja damara da kayan aikin da ya kamata, domin Nijar sai ta ga bayan wannan lamarin inji gwamnan na jahar Tahoua Issa Musa.
Labarun da ke fitowa daga wannan yankin, suna cewa, askarawan na Nijar a lokacin wannan kazamar karawa da yan ta'adda da suka so su arce zuwa kasar Mali a lokacin suka ji ba dadi, inda su ka shafe su gaba daya.
Muryar Amurka ta tuntubi Sidi Mohamed Sidi shugaban gidan rediyon karkara na Tchintabaraden da ke iyaka da gundumar Tilliya inda ya tabbatar da gaskiyar lamarin game da abinda ya wakana a lokacin wannan harin na ‘yan ta'adda.
Yanzu haka hukumomin jamhuriyar Nijar, sun kara aika sojoji a cikin motocin yaki masu sulke kuma a cikin damara zuwa wannan iyakar domin tabbatar da irin lamari da ‘yan ta'adda suka saba kar ya sake abkuwa.
Saurari rahoto cikin sauti daga Harouna Mamane Bako: