A Jamhuriyar Nijar, shugaban kasa Bazoum Mohamed ya halarci hawan Idin babban sallah, a Massalacin El Kadafi a Babban Birnin Yamai tare da shugaban majalisar dokoki ta kasa Seyni Omar da Fara-minista Uhumudu Mahamadu.
Sauran wadanda suka halarci hawan idi sun hada da ministoci da 'yan majalisun dokoki na kasa da shugabanin hukumomi na kasa yayin da dubun - dubatar al'ummar Musulmi suka gudanar da hawan idin Babbar sallah a ko'ina a fadin kasar.
A garin Birni N'Konni, bayan hukumomi na bariki da na gargajiya sun isa massalacin idin, sai Liman Amadu ya iso da misalin karfe 9 na safe inda a ka soma sallar.
Bayan kamalla sallar, sai a ka yanka ragon liman domin baiwa sauran Musulmi damar yin yankan sallar don koyi da Annabi Ibrahima kamin daga bisani Alhadji Ibrahim Abba Lele shugaban gundumar Birni N'Konni shiwa jama'a jawabi kan mahimmancin wannan babban ranar.
Daga bisani, magajin garin Birni N'Konni Abdu Mahamidu ya ja hankullan matasa da su tafi a hankali da kuma kula yayin da suke komawa gida kan ababen hawa bayan an kammala wadanan shagulgullan babbar sallah.
Yanzu haka dai a dukkan fadin kasar ta Nijer, ana cigaba da gashin tarunan dabbobin da musulmin suka yanka, kamin gobe da safe su shiga zuwa rabon nama wa makabta da ma yan uwa da aminan arziki yayin da yara kankana ke zagayawa domin neman barka da sallah.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: