Kalamun kakakin majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar, Usseini Tinni, na ci gaba da shan suka daga jam'iyyun adawa.
Ya yi jawabin ne a lokacin kamalla aikinsu na shekaru 5, a matsayin 'yan majalisa, inda yake cewa "ai zabe ya kare, don sabbin 'yan majalisun da za su kama aiki a ranar 17 ga wannan watan na tsawon shekaru 5, masu zuwa da za su ci gaba da ayyukan cigaban kasa, da ceto al'ummar."
Sai dai 'yan adawa na cewa, tsohon kakakin majalisar da ta kammala aiki ba shi da hurumin yin wadannan kalaman, domin kotun tsarin mulki tana iya cewa a sake zabe a wadansu wurare, in ji shugaban jam'iyar RDR Canji reshen Birni N'Konni, Mahamane Usmane.
Amma a Jam'iyar PNDS Tarraya mai mulkin kasar, Alhadji Dan Baba Maman Ceni, ya ce suna cike da mamakin wannan zancen da 'yan adawa suka kawo a wannan lokacin, don kuwa ai an gama zabe, yanzu kawai ana jiran sakamako ne daga kotu.
Ita dai majalisar dokoki ta kasa da Usseini Tinni ya jagoranta ta riga ta kammalla nata aikin na shekaru 5, 'yan kasar da Allah zai yiwa tsawon rai za su kalli yanda sabuwar majalisa zata nada nata kamun ludayi a tsawon shekaru masu zuwa.
Ga rahoton Haruona Mamane Bako a cikin sauti.