Masu neman shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican suna takara yau Talata, yayinda kuri'ar neman jin ra'ayin jama'a take nuna cewa Donald Trump, zai iya kara tazara da yake baiwa abokan takararsa domin neman tikitin takarar karkashin jam'iyyar.
Jihar Michigan ce take da wakilai 59 mafi yawa. 'Yan takara zasu sami wani kaso daga cikin wakilan, gwargwadon yawan kuri'u da dan takara ya samu a zaben na yau Talata, kamar yadda zasu yi kan delegates 91 da zasu samu a zabubbukan da za'a yi a jihohin Mississippi, da Idaho, da Hawaii.
Gabannin zaben na yau Talata, Donald Trump, yana gaban senata Ted Cruz da wakilai 82, yayinda Sanata Marco Rubio da Gwamnan jihar Ohio John Kasich suke can baya. Suna fatar taka muhimmiyar rawa a zaben da za'a yi makon gobe a jihohinsu.
A bangaren 'yan Democrat kuma, ana zabukan ne a jihohi Michigan da Mississippi. Tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta wuce Sanata Bernie Sanders a ra'ayoyin jama'a.