Sakamkon kuri'ar neman ji ra'ayon jma'a na baya bayan nan, ya nuna Trump yana kan gaba da sauran abokanan takararsa da kamar kashi 40 cikin dari, yayinda 'yan majalisar dattjai biyu Marco Rubio da Ted Cruz, suke fafatawa na zama na biyu, ko wanne daga cikinsu yana da kamar kashin 20 cikin dari.
Samun nasara a zaben da za'a yi yau a Nevada zai baiwa 'yan takara kwarin guiwa zuwa lokacin da za'a yi zabe ranar daya ga watan gobe, watau mako daya nan gaba, inda kusan sulusin jihohin Amurka zasu gudanar da zaben fidda dan takara.
Marco Rubio, wanda shi ba kamar Trump da Cruz ba, wadada sun sami nasarar lashe wasu jihohi, ya sami goyon bayan wasu jiga-jiagan jam'iyyar Republican gabannin zaben na Nevada, cikinsu harda tsohon senata kuma dan takarar shugabancin Amurka kuma Ted Cruz.