Sanatan na Vermont Mr Senders, ya doke abokiyar karawarsa hiliray Clinton, tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka da maki 60 yainda ita kuma ta sami maki 38. Haka shi ma Donald trump ya sami maki 35 a jam’iyyar ta sa ta Republican, wanda ke biye da shi shine gwamnan jihar Ohio John Kasik, wanda ya ba sauran ‘yan takarar tazara mai yawan gaske. Sakamakon wannan zaben na New Hampshire ya fidda raguwar ‘yan takarar na jam’iyyar republican, don tsohon shugabar kamfanin kere-keren kimiya Carly Fiona, wadda ta zo ta 7 a jerin ‘yan takarar da kuma gwamnan jihar New Jersey Chris Cristie wanda ya zo na 6 sun sanar da cewa sun janye daga takarar.
Wannan ya sa sauran ‘yan takarar da ke kan gaba fara duban zabe na gaba wanda za a yi ranar 20 ga watan nan, inda jam’iyyar republican za ta gudanar da zabe a south Carolina, ita kuma democrat za ta yi na ta a jihar Nevada da ke yammacin Amurka, jihar da tayi suna wajen chacha. Kwana 3 bayan wannan zaben kuma, jam’iyyar Republican za ta yi zabe a Nevada yayinda ita kuma democrat za ta yi a south Carolina wato ranar 27 ga wannan watan ke nan.