Gaba dayansu 'yan takarar suka fi maida hankali game da maganar tattalin arzikin kasar da kuma matsa kaimi wajen sa hannu don murkushe ‘yan ta’addar kungiyar ISIS. Dan takara Bernie Sanders yace, “bai kamata Amurka ta yi kamar ‘yar sandar duniya ba.
‘Yan ISIS abu ne da ya kamata a hada karfi da karfe da Rasha da kuma rundunar sojojin kasashen Musulmi. Ina son in fadawa Saudiyya ta zo a fuskanci ISIS maimakon yaki a Yemen. Qatar ta zo a yaki ISIS maimakon kashe Dalar Amurka Biliyan 200 a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya.
Itama Hillary ta goyi bayan sojojin taron dangin da ke kokarin murkushe ‘yan ta’addar ISIS ta hada kai da rundunar Sunni da Kurdawa, amma bata goyon bayan aika sojojin kasa na Amurka zuwa can wanda tace babban kuskure ne yin haka.
Tsohon gwamnan Maryland Martin O’Malley ma ya yi tsokacin ayyukan kungiyar kasashen Afirka ya kamata su yi a Somalia.