Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Dakatar Da Musayar Bayanan Sirri Tsakaninta Da Ukraine


Daraktan hukumar leken asirin Amurka (CIA) John Ratcliffe
Daraktan hukumar leken asirin Amurka (CIA) John Ratcliffe

Ratcliffe yace dakatarwar a fagen daga dana musayar bayanan sirri ta wucin gadi ce, kuma yana sa ran cewar Amurka za ta koma aiki kafada da kafada tsakaninta da Ukraine a nan gaba.

Amurka ta dakatar da musayar bayanan sirri tsakaninta da Ukraine bayan lalacewar alaka tsakanin Kyiv da fadar White House, kamar yadda daraktan hukumar leken asirin Amurka (CIA) John Ratcliffe ya bayyana a yau Laraba.

Shugaba Donald Trump da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky sun yi musayar cacar baki a bainar jama'a a ofishin shugaban Amurka a makon da ya gabata, abin da ya sabbaba babbar kawar Ukraine din dakatar da agajin sojin Amurka mai matukar mahimmanci.

Ratcliffe ya tabbatar da dakatar da musayar bayanan sirri ne yayin da Ukraine ta nemi a kwace yankunan da Rasha ta mamaye.

"Shugaba Trump na da tambaya ta zahiri a kan ko da gaske Shugaba Zelensky ya ke shirin wanzar da zaman lafiya," kamar yadda Ratcliffe ya shaidawa shirin kasuwanci na tashar talabijin ta Fox.

Ratcliffe yace dakatarwar a fagen daga dana musayar bayanan sirri ta wucin gadi ce, kuma yana sa ran cewar Amurka za ta koma aiki kafada da kafada tsakaninta da Ukraine a nan gaba.

Ga rundunar sojin Ukraine mahimmancin bayanan sirrin Amurka daidai yake dana makamai a mummunan yakin da take gwabzawa da Rasha kuma dakatar da agajin yazowa dimbin talakawan Ukraine da matukar mamaki.

Mashawarcin shugaban Amurka akan harkokin tsaro Michael Walz ya shaida wa manema labarai a fadar White House cewar "mun dan dakata ne mu sake nazari akan dukkanin bangarorin dangantakarmu."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG