Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya jagoranci wasu jami’an Fadar White House uku a wata ziyarar da suka kai ranar Laraba zuwa wani muhimmiyar iyakar Texas da Mexico, inda ya jaddada matsayar Shugaba Donald Trump kan tsaurara matakan shige da fice tare da tabbatar wa da Amurkawa cewa dakarun kasar ba su da shirin mamaye Mexico.
Ziyarar zuwa karamin garin Eagle Pass da ke kan iyaka a Texas, na zuwa ne bayan jawabin da Trump ya gabatar a gaban Majalisar Dokoki a daren Talata, inda ya bayyana shirin kamawa da korar baki da kalmomin “fitar da su da kuma yin hakan da sauri.”
Maganganun Vance sun kuma biyo bayan matakin Trump na ayyana kungiyoyin masu safarar miyagun kwayoyi a matsayin kungiyoyin ‘yan ta’adda na kasa da kasa.
"Ba zan yi wata sanarwa game da wani shiri na mamaye Mexico a nan yau ba," in ji Vance. "Shugaban kasa na da iko mai karfi, tabbas, zai yi magana kan wadannan batutuwa yadda ya ga dama. Amma abin da kungiyoyi masu safarar miyagun kwayoyi suka tilasta mu yi shi ne yin amfani da dukkan albarkatun sojojin Amurka domin aiwatar da tsauraran matakan kare iyaka."
Daraktan Leken Asiri na Kasa, Tulsi Gabbard, wacce ta raka Vance, ta jaddada hakan, tana mai cewa, "Manufarmu ita ce kare lafiyar ‘yan Amurka."
Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, wanda shi ma ke tare da Vance da Gabbard a Texas, ya nanata cewa yana ganin “tsaron iyaka tamkar tsaron kasa ne,” tare da yin bayani kan irin rawar da sojoji za su taka, duba da cewa doka ba ta ba su damar gudanar da ayyukan ‘yan sandan farar hula ba.
Dandalin Mu Tattauna