Daruruwan mutane ne suka taro a yankin Khan Yunis da ke kudancin birnin Gaza inda Hamas ta mika bakaken akwatunan gawa 4 ga kungiyar ba da agaji ta Red Cross, wacce ta yi safararsu cikin jerin gwanon motoci domin mikasu ga rundunar sojin Isra’ila.
Wata tawagar jerin gwano ta Isra’ila ta ratsa ta yankunan da mutane suka taru a gefen hanya rike da tutocin Isra’ila, sannan gawarwakin sun iso sa’o’i da dama daga bisani zuwa cibiyar binciken kwakwaf a fannin likitanci da ke birnin Tel Aviv domin tantance bayanan gawawwakin.
Mutanen da aka saki a yau Alhamis sun hada da mutum mafi kankantar shekaru cikin wadanda ake garkuwa dasu, jariri Kfir Bibas, wanda ke da watanni 9 lokacin da aka yi garkuwa da shi, sai dan uwansa mai shekaru 4, Ariel Bibas da kuma mahaifiyarsu, Shiri Bibas.
Dandalin Mu Tattauna