Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gaza: Isra’ila Za Ta Saki Fursunoni 602 Gobe Asabar


Wadanda za a sakin sun hada da, mutane 445 daga zirin Gaza da aka kama bayan harin da Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoba wanda ya haddasa yakin, 60 daga cikinsu na zaman gidan kaso na dogayen shekaru da 50 da aka yankewa daurin rai da rai, da 47 da aka sake kamawa bayan musayar fursunonin 2011

Isra’ila za ta saki fursunoni 602 daga gidajen kurkunta a gobe Asabar a wani bangare na musayar fursunoni tsakaninta da kungiyar Hamas karkashin yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza da ke gudana, a cewar kungiyar Falasdinawa masu fafutukar kare hakkin fursunoni.

Wadanda za a sakin sun hada da, mutane 445 daga zirin Gaza da aka kama bayan harin da Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoba wanda ya haddasa yakin, 60 daga cikinsu na zaman gidan kaso na dogayen shekaru da 50 da aka yankewa daurin rai da rai, da 47 da aka sake kamawa bayan musayar fursunonin 2011, kamar yadda kakakin kungiyar, Amani Saraneh ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Sarahneh ta kara da cewar fitar da mutane 108 daga cikin fursunonin zuwa wajen yankunan Isra’ila dana Falasdinawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG