Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Za Ta Mika Gawarwakin ‘Yan Isra’ila 4


A gobe Alhamis, kungiyar Hamas za ta mika gawawwakin Yahudawa 4 da take garkuwa da su a abinda ta bayyana da musayar fiye da fursunoni Falasdinawa 600, abinda zai kawo karshen gabar farko ta yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza.

Amurka ta bayyana cewa ana cigaba da tattaunawa akan gaba ta 2 ta yarjejeniyar tsagaita wutar wacce galibi an amince da ita saidai yanayin sarkakiya da tsawon lokacin aiwatar da ita sun bayyana irin raunin da take da shi.

A Isra’ila , dubban masu makoki ne suka hadu domin halartar jana’izar Shiri Bibas da ‘ya’yanta maza, wadanda aka kashe yayin da ake garkuwa dasu a Gaza kuma suka zamo wata alama ta irin wahalar da mutanen kasar da ake garkuwa da su suka sha.

Yarjejeniyar tsagaita wutar ta dakatar da yakin Isra’ila da Hamas wanda harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023 ya sabbaba, kuma ta bada damar sakin 25 daga mutanen da ake garkuwa dasu da ransu domin musayar daruruwan fursunoni.

Wani babban jami’in Hamas yace “musayar za ta gudana ne a lokaci guda”.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG