Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Ta Bukaci Isra’ila Ta Fara Aiwatar Da Gabar Gaba Ta Yarjejeniyar Gaza


Kungiyar Hamas ta bukaci al’ummar kasa da kasa su yiwa Isra’ila matsin lamba ta shiga gaba ta gaba ta yarjejeniyar tsagaita wutar da ta dakatar da yakin Gaza, yayin da masu shiga tsakani suka koma tattaunawa a birnin Alkahira.

A yau Juma’a, kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bukaci al’ummar kasa da kasa su yiwa Isra’ila matsin lamba ta shiga gaba ta gaba ta yarjejeniyar tsagaita wutar da ta dakatar da yakin Gaza, yayin da masu shiga tsakani suka koma tattaunawa a birnin Alkahira.

Yayin da ya rage sa’o’i a kawo karshen gabar farko ta yarjejeniyar sulhun, a jiya Alhamis, kasar Masar mai shiga tsakani ta bayyana cewar wakilan kasashen Isra’ila da Qatar da Amurka sun isa birnin Alkahira domin yin tattaunawa mai tsanani a kan gaba ta 2 da ya kamata ta dakatar da yakin a mataki na dindindin.

A Isra’ila, kwana guda bayan da rundunar sojin kasar ta amince da gazawarta wajen kare harin Hamas na 2023 da ya sabbaba yakin, yayin da masu makoki suka taru domin jana’izar Tsachi Idan, da ya daga cikin wadanda aka yi garkuwa dasu a Gaza da aka dawo da gawarsa.

Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa cewar “yayin da gabar farko ta yarjejeniyar tsagaita wuta ke karewa, muna kira ga al’ummar kasa da kasa su yiwa kasar Isra’ila matsin lamba ta gaggauta shiga gaba ta 2 ta yarjejeniyar ba tare da bata lokaci ba,” a cewarta.

A jiya Alhamis Firai Minista Benyamin Netanyahu “ya umarci tawagar masu shiga tsakani ta tafi alkahira”, kamar yadda ofishinsa ya bayyana jim kadan bayan da Hamas ta mika gawawwakin idan da wasu mutane 3 da ake garkuwa dasu a Gaza a karkashin yarjejeniyar, domin musayar daruruwan Falasdinawan dake tsare a hannun Isra’ila.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG