Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Zata Tura Tawagarta Zuwa Qatar Domin Ci Gaba Da Tattaunawar Tsagaita Wuta


Isra'ila da Bahrain
Isra'ila da Bahrain

A makon da ya gabata, Isra’ila ta matsawa Hamas lamba da ta sako ragowar mutanen da take garkuwa da su na karin lokaci a fuskar yarjejeniyar ta farko, wadda ta kare a karshen makon jiya da kuma daukar alkawarin shiga tattaunawar karshe.

Isra’ila ta ce zata tura tawagar wakilanta zuwa Qatar a ranar Litinin, a kokarin ci gaba da tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza, yayin da kungiyar Hamas da Amurka ta ayyana ‘yar ta’adda, ta nuna shawa’ar shiga tattaunawar tare da masu shiga tsakani daga Misra da Qatar a kan fara tattaunawar fuska ta biyu ta yarjejeniyar tsagaita wuta dake fuskantar jinkiri.

Sanarwa daga ofishin Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu bata yi wani karin bayani ba sai dai kawai ta ce “ta amince ne da gayyatar masu shiga tsakanin masu samun goyon bayan Amurka.” Kakakin Hamas Abdel-Latif al-Qanoua shima bai yi karin bayani ba. Wata daya kenan da aka jinkirta tattaunawar fuska ta biyun.

Babu wani karin haske nan da nan daga fadar White House, wadda ta tabbatar a ranar Laraba cewa ta yi tattaunawa da Hamas kai tsaye, lamarin da ya zo da al’ajabi.

A makon da ya gabata, Isra’ila ta matsawa Hamas lamba da ta sako ragowar mutanen da take garkuwa da su na karin lokaci a fuskar yarjejeniyar ta farko, wadda ta kare a karshen makon jiya da kuma daukar alkawarin shiga tattaunawar karshe. Ana sa ran Hamas har yanzu tana rike da mutane 24 da kuma gawarwaki 34.

A karshen makon da ya gabata ne Isra’ila ta katse duk wasu kayayyaki da ake kaiwa Gaza da kuma al’ummarta fiye da miliyan biyu yayin da ta matsa wa Hamas lamba ta amince da shiga tattaunawar yarjejeniyar. Hamas ta ce matakin zai shafi sauran wadanda take garkuwa da su.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG