Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afrika Ta Kudu Ta Zargi Isra'ila Da Amfani Da Makamin Yunwa A Gaza


Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa

A yau Laraba, Afrika ta Kudu tayi tir da takaita shigar da kayan agaji zuwa zirin Gaza da yaki ya daidaita da Isra'ila ke yi tun a karshen makon da ya gabata, inda tace hakan tamkar amfani da yunwa ne a matsayin makamin yaki.

Kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wutar da ke aiki tun cikin watan Janairun da ya gabata, ta taimaka wajen karuwar shigar da kayan agaji zuwa Gaza, kafin Isra'ila ta sanar a Lahadin da ta gabata cewa ta dakatar da shigar da kayan har sai kungiyar Hamas ta amince da sharudanta na tsawaita yarjejeniyar sulhun.

"Hana shigar da kayan abinci zuwa Gaza ci gaba da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki da Isra'ila ke yi a wani bangare na ci gaba da yakin da ta ke yi a hukuncin da kotun duniya ta bayyana da kisan kare dangi akan al'ummar Falasdinawa," kamar yadda ma'aikatar wajen Afrika ta Kudu ta bayyana a wata sanarwa, inda ta ke tsokaci a kan karar da Pretoria ta shigar a kan Isra'ila da ke gaban kotun duniya.

"Al'ummar Gaza na cikin matukar wahalhalu kuma suna bukatar agajin kayan abinci da matsugunai da magunguna cikin gaggawa," kamar yadda sanarwar ta bayyana.

"Afrika ta Kudu ta bukaci al'ummar kasa da kasa su tuhimi Isra'ila," a cewar sanarwar.

Yayin da Isra'ila ke cewar ta na son tsawaita gabar farko ta yarjejeniyar tsagaita wutar zuwa tsakiyar watan Afrilu, kungiyar Hamas wacce ta haddasa yakin Gazan da harin da ta kaiwa Isra'ila a watan Oktoban 2023- ta dage a kan tsallakawa zuwa gaba ta 2, wacce za ta kawo karshen yakin a matakin dindindin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG