Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cikin Fargaba A Gaza Yayinda Isra’ila Ta Hana Shiga Da Kayan Tallafin Jinkai


Manyan motoci dauke da kayan tallafin jin kai
Manyan motoci dauke da kayan tallafin jin kai

A ranar Asabar ne kashin farko na yarjejeniyar tsagaita wutar ya kare, inda kungiyar mayakan Hamasa da Isra’ila da Amurka suka ayyana da kungiyar ta’addanci ke tababar yadda kashi na biyu na yarjejeniyar zai kasance.

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi a ranar Litinin cewa, kudurin Isra’ila na dakatar da shiga da tallafin jin kai in banda ruwa kadai zuwa cikin zirin Gaza zai gaggauta haifar da mawuyacin hali ga yara da iyalai dake fafutukar tsira da rayuwa.

Daraktan yanki na Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya, Edourd Beigbeder ya ce, hana shiga da tallafin da aka sanar a jiya zai haifar da gagarumar matsala ga aiyukan ceton rayukan farar hula, don haka wajibi ne kuma abu mai muhimmanci ga rayuwar yara a kiyaye da sharrudan dakatar da yakin da aka cimmawa da bayar da damar shiga da kayayyakin agaji cigaba da shiga yankin ba tare da wata tsangwama ba.

A ranar Asabar ne kashin farko na yarjejeniyar tsagaita wutar ya kare, inda kungiyar mayakan Hamasa da Isra’ila da Amurka suka ayyana da kungiyar ta’addanci ke tababar yadda kashi na biyu na yarjejeniyar zai kasance.

A ranar Lahadi, Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce, jakadan Amurka a Gabas ta Tsakiya Steven Witcoff ya bayar da shawarar kara wa’adin tsagaita wutar har zuwa 20 ga watan Apirilu, wanda zai sarara ma watan Ramadan da kuma lokacin hutun yahudawa. A lokacin ne kuma Hamas zata saki rabin waadanda take garkuwa da su a rana ta farko, sauran kuma a sake su da zaran an cimma yarjejeniyar tsagaita wutar ta din din din.

Firai Minista Netanyahu ya fada ta wani sakon video cewa, shi ya amince da Shirin, amma Hamas ta yi watsi da shi.

Daga nan ne ya ce, gwamnatin sa zata dakatar da bari ana shiga da kayayyaki cikin Gaza, da zargin Hamas da hana Falasdinawa samun kaiwa ga kayayykin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG