Yau ya cika kwanaki dari da aka sace ‘yan matan makarantar Chibok dake jihar Borno a arewa maso gaashin Najeriya.
Kuma yau ne shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya gana da iyayen yaran da aka sace da kuma wadanda suka samu kubuta daga hannun ‘yan Boko Haram, a fadan Gwamnati a Abuja.
Kafin ganawar ta yau shugaban ya tattauna da gwamnan jihar ta Borno Malam Bukar Shettima, da wasu jami’an gwamnati domin duba hanyoyin da za’a tallafawa iyaye da yaran da suka kubuta daga hannun ‘yan Boko Haram.
Da kuma irin shirye-shiryen da gwamnati ta keyi na tabbatar da cewa ta kubutar da sauran ‘yan matan sama da dari biyu da har yanzu suke hannun ‘yan Boko Haram.