Kungiyar dai tace ta sami wannan kididdiga ne tun daga watan Janairu zuwa watan Afrilun wannan shekara, duk da yake kungiyar ta bayyana cikin shafinta na yanar gizo cewa basu da sahihin tabbaci game da wannan bayanai da suka wallafa. Tace andai jibge gawarwakin mutanen ne a dakunan ajiye gawarwaki dake cikin asibitoci a garin Maiduguri.
Daga bisani aka binne su a wasu makabarta, wanda kuma tace akwai bukatar daukar matakan gaggawa. Haka kuma kungiyar tayi zargin cewa akwai kananan yara 12 wanda suka hada da mata da jarirai 4 da basu kai shekara guda ba.
Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda, ya tuntubi Birgediya janal Rabe Abubakar, mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, inda yace, “Gaskiya lamari abin ya bamu juyayi, saboda bayan wadannan mutane sun fito da nasu rahoto kwanakin baya, muka gayyacesu domin su ga inda muke ajiye mutanen, har suka bamu shawarwari masu kyau har muka dauka muka kuma gabatar da duk abinda suka shawarcemu.” Ya ci gaba da cewa sai gashi daga baya sun fitar da wannan rahoto.
Daga karshe Birgediya Rabe, yace wannan makirci ne irin nasu kuma ba mamaki wani buri suke son su cimma, amma su a masayinsu na jami’an tsaro da sojojo suna nan suna kokarin tabbatar da cewa yadda sukayi kokarin shiga Dajin Sambisa, to suna son kawo karshen wannan yaki da nasara.