Wadanda suka yi korafi sun nemi shugabannin kasar su yi masu adalci domin idan ba'a yi masu adalci ba, ba zasu ji dadi ba tare da kiran shugaba Buhari da ya duba lamarin ya tausayawa talakawa.
Kungiyar dake rajin kare muradun arewa wacce ta fara zanga zangar kyamar janye tallafin man fetur lokacin da gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi yunkurin yin hakan a shekarar 2012 tace ko yanzu ashirye take ta kira gangamin zanga-zangar.
Barrister Audu Bulama Bukati shugaban kungiyar yace a fahimtarsa karin farashin man fetur abun takaici ne. Yace abu na farko duk wadanda suke cikin wannan gwamnatin ta Buhari da su suka yaki yunkurin janye tallafi zamanin gwamnatin Jonathan.Bugu da kari sun kara farashin yanzu ba tare da tuntubar mutane ba kamar yadda gwamnatin Jonathan ta yi. Kamata ya yi su yiwa 'yan Najeriya bayani akan hujjar cire tallafin kafin ma su yi hakan. Suna ganin shugaba Buhari ya dauki 'yan Najeriya ba bakin komi ba.
Bukati yace abu na biyu lokacin da aka cire tallafin bai dace ba saboda ana cikin matasla. Farashin dala ya tashi a cikin Najeriya. Farashin abinci da na masarufi sun tashi. Ya kira fadar shugaban kasa ta fito ta yiwa 'yan kasa bayani dalla dalla dalilin da suka janye tallafin.
Ga karin bayani.