Dan Majalisar Wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Balanga da Billiri Hon Ali Ishaq, ya shaidawa wakilin Muryar Amurka, Abdulwahab Mohammad, cewa ranar Talatar makon gobe zasu kawo batun domin nemawa ‘yan Najeriya sauki. Har ma ya nuna cewa babu wanda ya tuntubesu kafin zartar da wannan hukunci.
Sai dai kuma a gefe guda wasu mutane na ganin cire tallafin na da alfanu, kamar yadda Abdulwahab Adamu na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, yace yana goyon bayan cire tallafin Mai domin babu yadda ba a yi ba Mai yaki wadata sai gashi daga cire tallafin mutum zai iya shiga gidan Mai ya saya ba tare da matsala ba.
Siyasar hawa da saukar farashin Man fetur a Najeriya, ya faro ne tun daga zamanin mulkin Janaral Yakubu Gawon, tun wannan lokaci duk shugaban kasan Najeriya da yah au kan mulki sai ya bullo da irin nasa farashin.
Domin karin bayani.