Tare da kuma samun wakilai na Amurka da Birtaniya da Equatorial Guinea da tarayyar Turai da kungiyar Afirka ta Yamma da kungiyar bunkasa cinikayya ta Afirka ta Tsakiya da hukumar kula da yankin Golf of Guinea. Baki daya zasu halarci wani babban taro a Abuja na tsaro, domin daukar matakan karshe kan aiwatar da nasarorin da aka fara samu akan yaki da kungiyar Boko Haram, da tsara manufofin zaman lafiya tsakanin al’ummar Najeriya da bunkasa cinikayya da kasuwanci.
Kamar yadda sanarwar gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar, baban muhimmin batu a taron shine daukar matakai na gaggawa wanda zasu kawo karshen matsalolin ‘yan gudun hijira da sake tsugunnar da Miliyoyin mutanen da yaki da Boko Haram ya rabasu da mazaunansu. Tare da tsara hanyoyin da zasu ci abinci da kuma sake gina yankunansu.
Haka kuma za a yi amfani da taron wajen tsara wasu manufofi tsakanin Najeriya da Faransa, na inganta cinikayya da mu’amula ta al’adu na gargajiya da kuma harkokin tsaro. Bisa ga yadda aka tsara wannan taron shugaba Buhari zai fara ganawa ne da shugaban Faransa a fadar gwamnati.
Wanann taron dai ya zamanto na biyu bayan na farko da akayi a kasar Faransa wanda Francois Hollande ya jagoranta. Inda aka fara tsare tsaren da zasu kai ga samun nasarar yaki da kungiyar Boko Haram da sake tsugunnar da wadanda yaki raba da muhallansu, sai kuma bunkasa cinikayya da kasuwanci tsakanin Najeriya da sauran makwabtan kasashenta da Faransa.
Domin karin bayani.