Rahotanni na cewa kungiyar Boko Haram na amfani da dabarar baiwa matasa rancen kudi domin yin kasuwanci, daga bisani kuwa duk wanda ya karbi kudin kan koma kungiyar. Kamar yadda rundunar sojan Najeriya ke gargadi ‘yan kungiyar na amfani da wasu dabaru domin yaudarar jama’a.
A cewar mukaddashin kakakin rundunar sojan Najeriya, Kanal Sani Usman Kuka Sheka, “A koda yaushe ‘yan ta’adda na Boko Haram na bullo da dabaru kala kala, musamman ma da yanzu anci karfinsu basu da wata nasaba. Amma duk da haka akwai kanbararru tsakaninsu wanda har yanzu basu bar wannan akida ba, suna bullo da dabaru da dama da suke cuta da yaudarar jama’a….”
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar ko a baya kafin kwace garin Mobi, dake zama cibiyar kasuwanci a jihar Adamawa, sai da ‘yan kungiyar suka raba takardun bayar da rancen kudi, inda ake tarkon matasa.
A cewar wani matashi da aka nemi bashi irin wannan rance, yace suna shigowa gari su tara matasa suce suna son su taimaka musu da jari domin gwamnati ta kasa, su zasu baiwa matasa bashi don suyi kasuwanci ko noma ko kuma kiwo. Da zarar mutum ya karba shikenan sai yadda Allah yayi.
Yanzu haka dai hukumomi sun dukufa wajen fadakar da al’umma kan abubuwan da ke faruwa a yanzu. Kaftin Adamu Yahaya Gulda, dake zama mukaddashin kakakin rundunar soja ta 23 dake Yola, ya bukaci jama’a musamman matasa da su kwana da sanin cewa idan wani mutum ya tunkaresu ba tare da sun san kowaye bay ace zai taimaka musu, su sanar da hukuma.
Domin karin bayani.