Shugaban amintattu na kungiyar dillalen man fetur na kasa Alhaji Baba Kano Jada yace basu ki a kara kudin ba amma karin na yanzu ya yiwa mutane yawa domin ba zasu ji dadinsa ba saboda ya kauce misali, ba'a yishi kan ka'ida ba.
Alhaji Jada yace babbar bulala ce da zata shafi kowa a duk fadin kasar. Yace akwai tallafi iri iri kamar idan an shigo da kaya, wato mai daga waje akwai kudaden da gwamnati ke biya wannan shi ne tallafi.
Shi ma shugaban ma'aikatan kananan hukumomi kuma ma'ajin kungiyar kwadago ta kasa Ibrahim Khalil ya bayyana karin tamkar tsumangiyar kan hanya ce fyadi yaro, fyadi babba. Yace duk wanda ya san abun da gwamnati take nufi a shirin ya san akwai lauje cikin nadi. Karin da gwamnati ta yi ba daidai ba ne kuma karya ce. Yace idan aka yadda da abun da gwamnati tayi 'yan kasuwa zasu fita su sayi dala su sayo man fetur daga waje. Yace ko yau dala ta tashi.
To saidai shugaban kwamitin raba man fetur na majalisar wailai Danlami Kurfi yace karin kudin ne zai magance matsala da kuma karancin man da kasar ke fama dashi. Yace an yi ne domin tattalin arzikin kasar ya bunkasa. Kafin aikin noma da ma'adanai ya kankama gwamnati tana son man fetur ya wadatu a kasar.
Ga karin bayani.