Shugaban hukumar kula da hada hadar kasuwanci ta ruwa, ko Shippers' Council, Dr. Hassan Bello yace raya cibiyoyin saukewa da dibar anfanin manoman Najeriya da sauran kayayyakin kasuwanci domin saida wa a ketare, zai taimaka ainun wajen samun kudin shiga ga miliyoyin mutane.
Hassan Bello wanda yake magana kan cibiyar kasuwanci ta Funtua yace tshoshin da hukumarsa zata kafa, a sassa daban daban na Najeriya, tamkar tashoshin bakin teku ne na doron kasa, ga yankunan Najeriya da basa bakin tekun atilantika.
Dr. Hassan Bello yace tattalin arziki shi ne zai dauki hankalin mutane yanzu. A duba a ga abun da jihohi zasu yi su rage rashin aikin yi , su rage talauci kana su samu kudin shiga. Yace suna son a dinga kawo kaya tashar zuwa wasu tasioshi. Yin hakan, zai kawo masana'antu domin ba sai mutum ya je Legas ko Fatakwal ba, kafin ya yi odar kaya. Ana iya kawo kaya daga Ingila ko Jamus a saukar dasu ma 'yan kasuwa. Ita ma tashar jirgi ce domin duk albarkatun gona za'a kawosu tashar.
Kamfanin Umaru Muttalab ke gina tashar ta Funtua kuma tuni ya kawo ma'aikata daga Jamus da kayan aiki. Da zara an fara aikin, kasuwanci zai habaka. Mutane zasu samu abun yi, kuma da an gama ginata mutane zasu dinga zuwa daga sassa daban daban.
Masana tattalin arziki irinsu Yushau Aliyu Abuja na ganin fara anfani da kasafin kudi zai rage kunci a gajeren zango. Yace a yi hanzari a fitar da kudade a biya 'yan kwangila, a soma ayyukan da zasu zaburar da mutane, wato da zasu samarda aikin yi nan take. A samarda abun da zai taimaki noma da wuri da kuma masana'antu.
Ga karin bayani.