Jami'an tsaro a Najeriya sun ce barazanar kai hare haren 'yan ta'addar Boko Haram ta ragu kwarai a babbana birnin Abuja, amma har yanzu jama'a da dama na fama da wahalar da 'yan kungiyar suka jefa su. Wakilin muryar Amurka Nicolas Pinault ya kai ziyara a sabon sansanin 'yan gudun hijira dake Kuchogoro inda ya dauko wadannan hotunan.
Sabon Sansanin "Yan Gudun Hijira Dake Birinin Abuja Najeriya

1
Wani Yaro A Zaune Yana Kallon Babaar Sa A Yayin Da Take Kokarin Dauraye Kayan Sawar Su A Sansanin Kuchogoro, Abuja Najeriya.

2
Tantunan Da 'Yan Gudun Hijira Ke Kwana A Sansanin Kuchugoro, Abuja Najeriya.

3
Inda Ruwan Datti Ya Kwanta A Sansanin 'Yan Gudun Hijrar Kuchogoro, Abuja Najeriya.

4
Lami John Ta Tsere Daga Gwoza A Jahar Borno Bayan 'Yan Kungiyar Boko Haram Sun Kaima Kauyen Su Hari, An Yi Garkuwa Da Ita Har Na Kwanaki Goma Sha Biyar Byan Yayin Da Suka Harbe Ta A Kafa.