Zuwa yanzu dai za’a iya cewa shugaba Buhari bai samu cikas da sashen majalisa ba wajen kudurorin da yake turawa idan an kwatanata da sashen sharia da yake gani yana haddasa masa cikas.
Kama daga amincewa da nada mataimaka goma sha biyar, zuwa kasafin kudin bana da aka samu cin karon alkaluma duk da haka dai akasarin ‘yan majalisar nason wanyewa lafiya da sashen zartarwan.
Saurin samu beli da zargin hadin bakin Lauyoyi da alkalai, wajen rufawa wadanda ake zargi da almundahana asiri ya sanya shugaba Buhari bayanin dake nuna cewa ba zai bar wadanda ake tuhuma batare da tsatsauran hukunci ba.
Muhammadu Inuwa Yahaya, wani jigo a APC, yace wannan tsarin zai kai Najeriya ga gaci yana kuma mai cewa babbar matsalar mu cin hanci da rashawa ne kuma muddin aka dakile ta kashi 75 na matsalar Najeriya zai yi sauki da yardan Allah.
Gabanin nasarar zabe dai PDP, na gugar zana ga Buhari da cewa yana fuskar shanu wato yana tsumaiwa dake nuna cewa mawuyacin al’amari ne a iya bashi shawarwari ya dauka.