Duk kuwa da zargin saba yarjejeniyar daga bangaren gwamantin Syria. Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya bayyana cewa, masu sa ido daga Rasha da Amurka suna taro a biranen Geneva da Amman tun daga jiya Asabar, domin neman mafitar yadda za a kawo saukin rikicin Syria.
Kerry ya fada a Saudiyya cewa, daga bayanan da ake samu, rikicin na Syria ya rago da akalla kaso 80 zuwa 90, wanda hakan na da matukar muhimmanci in ji Sakataren wajen Amurkan.
Ministan harkokin wajen Syria Walid Muallem yace gwamnatinsu zata yi iya kokarinta kiyaye dokar tsagaita wuta amma ya nemi masu shiga tsakanin da su kara kwana 1 don jira isowar wakilan ‘yan adawa.