A sabon rahoton da suka fitar a jiya Juma’a, suka ce dukkan bangarorin mayakan sun aikata tsantsar ta’addanci akan farar hula a cikin dabara, tare da kaucewa daukar laifin da suka aikata.
Musamman a shekarar 2015 lokacin da sojojin ‘yan adawa suka yi rauni. Masu bincike na MDD sun gano cewa sojojin gwamnati da wasu matasa mayakan sa kan bangaren gwamnatin,
sun kai samame zuwa wasu kauyakun da suka yiwa kaca-kaca. Musamman ga wadanda basa goyon bayan gwamanatin kasar.
Babban Kwamishinan Kula da ‘Yancin Bil’adama na MDD Zeid Ra’ad Al’Husain yace, ko yawan rahoton fyade da cin zarafin da aka samu a Sudan din ya isa babban abin misalign da ya fi na ko ina a duniya.