A cikin wata sanarwar da suka fitar sa’o’I kadan bayan da kotun tsarin mulki ta tabbatar da sakamakon zaben 20 ga wannan watan, yan adawar suka dauki matakin kauracewa dukkan wasu harkokin da suka shafi tsare tsaren wannan zabe da ya hada da shugaba mai mulki Issoufou Mahamadou da Hamma Amadou dake tsare a kurkuku.
Alhaji Dudu Mahamadou na jam’iyyar MNRD HANKOURI na daga cikin kusoshin kawancen yan hamayya na COPA. Inda yace, “ba zamu halarci zaben nan ba bazamu yi wannan zaben ba, mun kira magoya bayan mu da kada su halarci wannan zabe. na biyu mun kirayi wakilan mu dake zauren majalisa munce su janye, mun kuma kirayi wakilanmu na hukumar zabe munce su janye. Saboda yadda akayi take-taken yin zaben, in kuma aka duba yadda hukumar zabe mai zaman kanta sai da ta dauki kwanaki biyar kafin ta fitar da sakamakon zabe, duba wannan kotun kolin da ta ki fito shi yadda aka sani kowa za a tara jama’a a ce ga abinda sakamako ya bada. Cikin dare ta fito da shi, shi kuma Issoufou kuma ya gudu da safe.”
Jam’iyyun na adawa sun kara kokawa akan abinda suka kira burus da korafe korafen da suka gabatarwa kotun tsarin mulki, inda suke ganin ya kamata kotu da duba amma ba a yi ba.
A nata bangaren jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki ta bayyana gamsuwa da hukuncin kotun tsarin mulkin kasar. Inda kuma suke ganin yan adawar a matsayin yan hamayyar da basu san kwanciyar hankali.
Sakamakon zaben na ranar 21 ga watan Fabarairu yayi nuni da cewa daga cikin yan takara 15 da suka nemi shugbancin kasa, dan takarar da yazo na biyu da na uku da na hudu dukkansu sun shiga zaben ne a karkashin inuwar jam’iyyun adawa.
Domin karin bayani.