Cruz, ya gayawa magoya bayansa a birnin Indianapolis cewa, "babu damar ya ci gaba, domin masu zabe sun gwammace wani."
Trump ya sami gagarumar nasara a zaben na jihar Indiana, senata Cruz yazo na biyu, sannan gwamnan jihar Ohio John Kasich yazo na uku.
Trump ya "yaba da irin nasarar da ya samu a jihar Indiana," daga nan ya yabawa Cruz,da kuma sauran 'yan takara su 15 wadanda ya kira gwarzaye masu basira. Daga nan yayi kira da a hada kai a jam'iyyar ta Republican.
Shugaban jam'iyyar Republican Reince Priebus, ya kira Trump a zaman "dan takarar jam'iyyar mai jiran gado".
Amma wani kakakkin gwamnan jihar Ohio wanda yake takara har yanzu yana cewa, gwamnan har yanzu yana ganin za'a fafata a dandalin babban taron jam'iyyar a watan Yuli, inda yake ganin zai sami nasara idan zabe yaje zagaye na biyu.
A bangare 'yan Democrats kuma, an ayyana senata Bernie Sanders, ya doke madam Hillary Clinton a zaben na Indiana.
Duk da nasarar da Sanders ya samu a jihar Indiana, Clinton tana gaba dashi nesa ba kusa ba a yawan wakilai, kuma kusan za'a iya cewa da wuya ace ya cimmata.