Dan takarar shugabancin Amurka na sahun gaba a Jam’iyya Republican Donald Trump yayi Allah wadai da wannan magana ta kamfanin, inda yace wannan abin kunya ne, kasancewar kamfanin zai kwashe damar samun aikin Amurkawa ya kai wata kasa ta daban.
Wannan dai ba sabon al’amari bane ga Trump, da dama ya fada tun a farkon bayyana maganar takararsa a watan Yunin bara, lokacin da yace, zai janye maganar cewa Ford bas a biyan ko kwabo wajen shigo da kayansu zuwa Amurka. Damar da suka samu daga yarjejeniyar kasuwancin Amurka ta Arewa.
Trump yace, duk wata mota ko na’urar da aka kera kamfanin da ke waje, to tabbas sai sun biya akalla harajin kaso 35 daga cikin 100 don shigowa da kayan zuwa nan cikin Amurka. Dan takarar Democrat Bernie Sanders ya sha kushe abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton game da wannan doka ta rashin biyan harajin shigo da kaya, duk da yake dai ita ta nuna kin abin daga baya wanda a da ta amincewa lokacin tana Sakatariyar wajen Amurka.