Zaben da za a ayi a gobe Talata idan Allah ya kaimu, tsakaninsa ne da babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar wato Ted Cruz.
Ana kallon idan har Trump yayi nasara a jihar Indiana to haka ya dada basa damar samun zama dan takarar Republican.
Kafin gangamin tsaida dan takarar da za su yi a birnin Cleveland na jihar Ohio a watan Yuli mai zuwa.
Bisa wasu kuri’un jin ra’ayin jama’a da aka gudanar sun nuna Donald Trump na gaba da maki 15 a jihar ta Indiana.
Wasu daga cikin ‘yan gani kashenin Trump a jihar Indiana sun ce, Donald ya kosa ya gama da wadannan zabuka domin ya fara kamfe na zaben kasa gaba daya.
Inda suka ce zai yi nesa da abokan hamayyarsa na jam’iyyar, wato Sanata Ted Cruz da Gwamnan jihar Ohio John Kasick.
Idan har Trump yaci jihar ta Indiana aka kuma hada da nasarorin da ya samu a jihohi 5 na gabashin Amurka, to hakan zai dada masa kwarin gwiwar samun tikitin jam’iyyarsu a gangamin na watan Yulin mai zuwa.
Ted Cruz ya matsu matuka da son lashe zaben fidda gwamnin na jihar Indiana, saboda hakan zai hana Trump samun yawan wakilan da ya kamata ya samu kafin ranar gangamin jam’iyyar Republican.