Majalisar ta ba da wa’adin makonni uku don kammala binciken a kuma gabatar mata da rahoto kan lamarin.
A cewar NLC, abin takaici ne a ce gwamnati ta bar wani kamfani mai zaman kansa yana kayyade farashin mai a kasar.
“Kafin rasuwarsa, Alhaji Umar Shehu Idris dai yana rike da mukamin Mataimakin Magatakardan Majalisar Masarautar Zazzau.” Sanarwar da masarautar ta fitar ta ce.
Kyaftin din na Super Eagles shi ya zura duka kwallayen biyun da Pillars ta ci a wasan wanda aka tashi da ci 2-0.
Kwamishinan Watsa Labarai da Tsaron Cikin Gida na jihar, Farfesa Usman Tar, ya sanar da wannan shawarar rage bukukuwan ne a wata sanarwa a ranar Litinin.
A ranar Talata 1 ga watan Oktoba Najeriya ta cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai.
Shettima ya wakilci Shugaba Bola Tinubu ne a taron wanda aka yi a karo na 79 a birnin New York da ke Amurka.
A daren Alhamis hukumar kwallon kafar ta NFF ta fitar da wannan sanarwar.
A ranar Lahadi, hukumar INEC ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben jihar ta Edo, nasarar da PDP ta ke kalubalanta.
A wata sanarwa da ya fitar ta hannu kakakinsa Bayo Onanuga, Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga duk wanda bai gamsu da sakamakon zaben ba, ya bi hanyar da doka ta tanada don bin kadi.
Taron na bana za a gudanar da shi ne daga ranar 24 zuwa 28 ga Satumba, 2024 a birnin New York.
Najeriya ita ce ta shida a iya taka kwallo a nahiyar Afirka yayin da Libya take matsayi na 33.
Shugaban na Najeriya ya kuma yaba da yadda sauran ‘yan takara suka nuna dattaku yayin gudanar da zaben wanda ya ce an gudanar lami lafiya.
“Labarin Seaman Abbas Haruna mai cike da abin tausayi wanda aka nuna a shirin ‘Brekete’ ya sa kwamitin majalisar wakilai na sojin ruwan Najeriya ya shiga cikin lamarin da nufin bankado gaskiyar abin da ya faru."
Bidiyon ya nuna yadda matar Abbas Haruna mai suna Hussaina ta zayyana irin halin da mijinta ya shiga bayan da ya samu sabani da shugaban bataliyarsa lamarin da ta ce ya kai ga tsare shi har ma ya haukace.
Sai dai a wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar a ranar 15 ga watan Satumbar 2024, Ribadu ya nemi Aziegbemi da ya janye kalaman nasa inda ya kwatanta lamarin a matsayin “zuki ta malle”
'Yan takarar biyu sun yi musabaha a farko, suka tsaya a bayan mimbarinsu a wani dandamali a Cibiyar Kundin Tsarin Mulkin Kasa da ke Philadelphia, sannan suka fara caccakar juna.
Domin Kari